in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xinhua ya watsa bayanai game da ranar barkewar yakin adawa da harin Japan
2014-07-06 16:55:34 cri
Domin tunawa da barkewar yakin kin harin Japan da ya auku a kasar Sin shekaru 77 da suka gabata, kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua, ya watsa wani bayani na musamman da ya yi wa lakabi da ' Tunawa da tarihi, don kare yanayin zaman lafiya da adalci'.

Cikin wannan bayani dai, Xinhua ya nuna cewa, kamata ya yi a yi hattara game da daukar duk wani mataki na hari da wata kasa ka iya kaiwa wata, kana ya yi kira da a yi kokarin kare yanayin zaman lafiya da adalci a dukkanin fadin duniya, tare da tabbatar da wayewar kan jama'a da ci gaban su.

Cikin bayanin an bayyana cewa, bisa irin hasarar da kasar Sin ta yi a yakin kin harin Japan, ta fahimci cewa ba za a samu damar kare kai ba sai fa in har kasa ta samu ci gaba. Kana neman ci gaban tattalin arziki, na bukatar samun kwanciyar hankali, yayin da samun kwanciyar hankali ke da alaka da bukatar tabbatar da adalci a duniya.

Bisa wannan jigo ne dai kasar Sin ke kokarin kiyaye tsarin zaman lafiya na duniya, wanda aka kafa bayan babban yakin duniyar, wanda kuma jama'ar ta, da ta sauran kasashe daban daban wadanda ke rungumar zaman lafiya suka sadaukar da rayukan su kafin tabbatar sa. Manufar da kuma ke bada damar ci gaba da walwalar ga al'ummun duniya baki daya.

Bugu da kari bayanin nan Xinhua, ya nuna cewa a yayin da yanayin duniya ke sauyewa, hadin gwiwa, da cimma moriyar juna sun fara zama manyan manufofin da ake bi wajen gudanar da harkokin kasa da kasa, koda yake dai kasar Japan, wadda ta taba kai hare-hare kan kasashe da yawa, ciki har da kasar Sin ya yin yakin duniya na 2, har yanzu ba ta yi nadama kan laifukan da ta aikata ba.

Hasali ma dai Japan din na ci gaba da girmamawa wadanda suka aikata laifukan yaki, tare da kokarin kalubalantar sabon tsarin duniya na wanzar da zaman lafiya, lamarin da ya janyo tabarbarewar huldar dake tsakanin ta da Sin, gami da haifar da barazana ga yanayin zaman lafiya a duniya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China