An dai tambayi Qin Gang ne ra'ayin sa game da tsokacin da Abe ya yi a ranar 30 ga watan na Mayu, yayin taron tattaunawa na Shangri-La da ake gudanarwa a kasar Singapore. Cikin jawabin na Abe ya yi zargin cewa, wasu kasashe na yunkurin sauya halin da ake ciki yanzu haka. Ya mai kira ga kasashen duniya da su yi biyayya ga dokokin kasa da kasa, a yayin da suke gudanar da harkoki a teku, su kuma daidaita sabanin dake tsakanin su cikin ruwan sanyi.
Game da hakan Mr. Qin Gang ya ce, kasar Sin ta lura da bayanan da shugabannin Japan suka yi a kwanan baya, game da wasu kasashe. Kuma kamata ya yi Japan ta yi wa kasashen duniya cikakken bayani kan matakan da take dauka ta fuskar aikin soja da tsaro, ta kuma bi dokokin kasa da kasa, da ka'idojin raya huldar kasa kasa yayin da take daidaita sabani da sauran kasashe makwabtan ta, a fannonin mallakar yankuna da teku.
Mr. Qin ya kara da cewa kasar Sin, na fatan Japan za ta fuskanci tarihi yadda ya kamata, ta girmama hakikanin abubuwan da suka faru, ta kuma kaucewa rura wutar kiyayya, ta dauki matakan a-zo-a-gani wajen kawo wa yankin da take ciki zaman lafiya da kwanciyar hankali. (Tasallah)