Kisan kiyashin da mahara Japanawa suka yi a birnin Nanjing na kasar Sin a yakin duniya na biyu da kuma fyaden da sojojin Japan suka yi wa mata, munanan laifuffuka ne na cin mutuncin dan Adam da mahara Japanawa suka yi a yakin duniya na biyu, kamar yadda Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya fada yau ranar Jumma'a 17 ga wata a nan Beijing.
Hong Lei ya kara da cewa, kasar Sin ta kalubalanci kasar Japan da ta girmama yadda jama'ar Sin da na sauran kasashen da maharan Japan suka taba aikata irin wadannan munanan laifuffuka a wurin suka ji a zukatansu, ta kuma waiwayi tarihinta yadda ya kamata. (Tasallah)