Kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta kan wasu abubuwan da ke cikin sanarwar da kasashen Amurka da Japan suka bayar cikin hadin gwiwa, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang yau ranar Jumma'a 25 ga wata.
Qin Gang ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, inda ya ce, yin soke-soke kan wasu kasashe bisa ga wasu batutuwa ba zai taimaka wajen warware batutuwa masu muhimmanci da kuma tabbatar da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya ba.
A yau ne Amurka da Japan suka ba da wata sanarwar hadin gwiwa, inda Amurka ta ce, za ta tabbatar da tsaron yankunan kawarta Japan baki daya, ciki had da tsibirin Diaoyu, sa'an nan sun bayyana ra'ayoyinsu kan wasu batutuwan da suka shafi tekun gabashin kasar Sin da na kudancin kasar Sin.
Dangane da hakan, Qin Gang ya nuna cewa, tsibirin Diaoyu da kananan tsibiran da ke kewayensa, yankin kasar Sin ne tun fil azal. Babu wanda ko kuma babu abin da zai iya hana gwamnatin Sin da jama'ar Sin su kiyaye mulkin kan kasa da kuma cikakkun yankunan kasa.
Mista Qin ya kara da cewa, kasar Sin ta kalubalanci Amurka da Japan da su yi watsi da manufofin da suka taba aiwatarwa a cacar bakin da suka yi, kuma wajibi ne su girmama moriyar sauran kasashen da ke wannan yanki da kiyaye abin da zai kawo damuwarsu, a kokarin ba da taimako wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Ya ce, ya kamata su yi tunani a tsanake kan yadda za su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a yankin nan. (Tasallah)