in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping zai halarci bikin bude gasar Olympics ta matasa a birnin Nanjing
2014-08-11 20:37:32 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Litinin 11 ga wata cewa, shugaban kasar Xi Jinping zai halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta matasan kasar ta lokacin zafi karo na biyu da za a yi a birnin Nanjing a ran 16 ga wata.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qing Gang ya bayyana cewa, bisa gayyatar da shugaba Xi ya yi musu, shugaban kasar Burundi Piere Nkurunzinza, shugaban kasar Fiji Epeli Nailatikau, shugaban kasar Maldives Abdullah Yameen, shugaban kasar Montenegro Filip Vujanovic, shugaban kasar Singapore Tony Tan Keng Yan, firaministan kasar Vanuatu Joe Natuman, da kuma babban magatakardan MDD Ban Ki-moon za su halarci bikin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China