Sanarwar ta ce yadda kasar Sin ta shata wannan yanki na tsaron sararin samaniya ya dace da dokokin kasa da kasa, don haka bai kamata kasar Japan ta yi korafe-korafe kan batun ba. Sa'an nan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin sam ba za ta yarda da shirin kudurin da takwararta ta kasar Japan ta zartas dangane da batun ba.
Ban da haka, kwamitin ya nanata cewa, tsibirin Diao Yu da sauran kananan tsibiran dake kewayensa sun kasance cikin harabar kasar Sin tun fil azal, don haka ba wanda ke iya musunta ikon kasar Sin wajen mallakar tsibiran. Amma duk da haka kasar Japan ta sanya tsibirin Diao Yu cikin yankin tsaron sararin samaniya nata, abin da kasar Sin ba ta amince da shi ba ko kadan.
A karshen sanarwar, an bayyana cewa, matakan da kasar Japan ta dauka su ne ainihin sabani da halin kiki-kaka a yankin tekun gabas na kasar Sin. Don haka, an bukaci bangaren Japan da ta dakatar da matakan tsokana, don amfanawa kokarin kyautata huldar dake tsakanin bangarorin 2, da kiyaye kwanciyar hankali a yankin tekun gabas na kasar Sin. (Bello Wang)