An ba da labari cewa, ministan tsaron kasar Japan Onodera Itsunori ya gana da takwaransa na kasar Philiphines Voltaire Gazmin a ranar Asabar din da ta gabata 7 ga wata, inda bangarorin biyu ke ganin cewa, matakin da Sin ta dauka na kafa yankin shata sassan tsaron sararin samaniyar tekun Kudu zai haifar da rikici a yankin Asiya-Pacific. Inda a nasa bangare Onodera Itsunori ya yi kira ga kasashen duniya da su nuna rashin jin dadi kan lamarin.
Da yake maida martani game da wannan bukata Mr Hong a gun taron manema labarai Litinin din nan 9 ga wata ya ce, Sin na nan a kan matsayinta na tsaron kasar, don haka ko kusa ba za ta yarda a tsoma mata baki kan harkokin cikin gidanta ba. (Amina)