A ganawar da ya yi da manema labarai a Litinin din nan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Qin Gang ya bayyana cewa, kasar Sin na bukatar Japan ta yi gyara bisa ga kuskurenta a kan yadda take ma tarihi rikon bayan hannu, ta kuma daina yin ayyukan da za su kara dagula dangantaka, sannan ta yi abubuwan da ya kamata domin samun amincewar sauran kasashen yankin Asiya da ma duniya baki daya.
Mr. Qin ya ce halayyar shugabannin kasar ta Japan na ban girma da ma ziyarar wajen Ibadan Yasukuni wani abu ne da bai dace ba ko kadan na halayyar shugabannin a yadda ma suka dauki tarihi, don haka kasar Sin ta bayyana matsayinta a kan wannan dabi'a.
Ya ce dabi'un shugabannin Japan zuwa ga wajen Ibadar Yasukuni wanda nan ne makabartan wadanda suka yi yakin duniya na 11 yana nuna ko Japan za ta iya waiwayen tarihi, ta kuma nuna nadamarta game da cin zarafin da sojojinta suka yi ma jama'a lokacin yakin duniya.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin ya ce, yana da muhimmanci ga Japan da ta nuna matukar nadamarta sannan ta waiwayi tarihi a kan cin zarafin da sojojinta suka yi a lokacin wannan yaki domin ta sake gina da kuma inganta dangantaka tsakaninta da kasar Sin. (Fatimah Jibril)