Kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta kan wasu abubuwan da ke cikin sanarwar da kasashen Amurka da Japan suka bayar cikin hadin gwiwa, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang yau ranar Jumma'a 25 ga wata.
Qin Gang ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, inda ya ce, yin soke-soke kan wasu kasashe bisa ga wasu batutuwa ba zai taimaka wajen warware batutuwa masu muhimmanci da kuma tabbatar da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya ba.
A yau ne Amurka da Japan suka ba da wata sanarwar hadin gwiwa, inda Amurka ta ce, za ta tabbatar da tsaron yankunan kawarta Japan baki daya, ciki had da tsibirin Diaoyu, sa'an nan sun bayyana ra'ayoyinsu kan wasu batutuwan da suka shafi tekun gabashin kasar Sin da na kudancin kasar Sin.