in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta mai da martani game da ziyarar manyan jami'an Japan a Yasukuni
2014-01-03 16:18:17 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta nuna fatan cewa, ya kamata Japan ta hada kai da kasashen makwabtanta domin warware matsalolin da suka taba fuskanta a tarihi ta hanyar yin shawarwari.

A gun wani taron manema labaru da ta yi a ran 2 ga wata, ma'aikatar ta mai da martani ne game da ziyarar da ministan cikin gida na kasar Japan Yoshitaka Shindo ya kai a karo na shida ran 1 ga wata a haikalin Yasukuni, wurin da aka tunawa da wadanda suka aikata laifufukan yaki a lokacin yakin duniya na biyu guda 14.

A ran 26 ga watan Disamba na bara, firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya kai ziyara a haikalin ba tare da yin la'akarin da adawar kasashen duniya, sauran kasashen Asiya da jama'ar kasarsa ba. Matakin da ya tsanantar da dangantakar dake tsakanin Sin da Japan, da kuma Korea ta Kudu da Japan.

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka Marine Harf ta bayyana ran 2 ga wata cewa, a ganin Amurka, dangantaka mai kyau dake tsakanin kasa da kasa a yankin Asiya-Pacific na da amfani sosai ga zaman lafiya da karko, wanda kuma ya dace da moriyar kasashen dake wannan yanki, kuma ya dace da moriyar Amurka.

Bugu da kari, Madam Harf ta jaddada cewa, Amurka na kira ga Japan da ta warware matsalolin da take fuskanta ta hanyar da yin shawarwarin diplomasiyya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China