An labarta cewa, akwai bayanai ko shaidu kimanin dubu 100 kan harin da Japan ta kaiwa kasar Sin a dakin adana bayanan tarihi na lardin Jilin, a cikinsu kashi 90% an rubuta su ne da harshen Japananci. An kasa wadannan bayanai zuwa kashi hudu, wato bayanai kan hukumar ba da jagoranci ta rundunar sojan Kantogun, da bayanai kan babban bankin yankin da Japan ta kafa a arewacin Sin, da bayanai kan fina-finai, da kuma wasu zane-zanen muhimman gine-gine dake birnin Xinjing, hedkwatar yankin da Japan ta kafa mallaka a lokacin a arewacin Sin.
Rukunin masana ya bayyana cewa, dakin adana bayanan tarihi na lardin Jilin yana da irin wannan bayanai da yawa, mafiya yawansu kuma na Japan ne yayin da sojojinta suke kai hari a Sin, wadanda suka bayyana irin munanan ayyukan da Japan ta yi a lokacin, wadannan sun kasance tabbatattun shaidu masu karfi kan kai hari a Sin da sojojin Japan suka yi. (Fatima)