in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kafa wata dokar tunawa da ranar nasarar yakin kin harin Japan
2014-02-26 16:14:05 cri
Sin za ta kafa wata doka don ayyana ranar 3 ga watan Satumba a matsayin ranar tunawa da ranar cimma nasarar yakin kin harin Japan, tare da mai da ran 13 ga watan Disamba a matsayin ranar tunawa da kisan kiyashin birnin Nan Jing.

A yammacin ranar 25 ga wata, a gun taro karo na 7 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12 aka zartas da daftarin shirin tabbatar da wadannan ranaiku biyu.

Game da bayani kan daftarin shirin kafa ranar tunawa da kin harin da sojojin Japan suka yiwa yankunan kasar Sin, an jaddada cewa, an bullo da wannan shiri ne domin tunawa da mazan jiya wadanda suka sadaukar da kai a cikin yakin da wadanda suka ba da gudunmawa, ta yadda za a bayyana muhimmiyar rawar da jama'ar kasar Sin suka taka a kokarin kin harin da aka kai musu da yaki da masu ra'ayin fin karfi, tare kuma da bayyana niyyar Sinawa na kare ikon mulkin kasa, cikakken yankinta da tabbatar da zaman lafiyar duniya.

Game da kebe ranar tunawa da wadanda aka halaka a kisan kiyashin da aka yi a birnin Nanjing, an yi bayani cewa, ta wannan hanya ba za a iya mantawa da illar da yake-yake suka jawowa jama'ar duniya musamman ma Sinawa ba, tare kuma da bayyana aniyyar Sinawa na yaki da hare-hare, da kiyaye hakkin Bil Adam, da kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a duniya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China