in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sukar da kasar Japan take yi wa kasar Sin wani abu ne da ba ya da makama, in ji ma'aikatar tsaro ta Sin
2014-08-11 16:27:05 cri
Ranar 10 ga wata, ma'aikatar harkokin tsaro ta kasar Sin ta ce, sukar da kasar Japan take yi wa sojojin kasar Sin, a cikin sabuwar takardar bayani da ta bayar kan aikin tsaron kasa, wani abu ne da ba ya da tushe balle makama.

Majalisar dokokin kasar Japan, ta amince da takardar bayani kan aikin tsaron kasar ta shekara ta 2014 a ranar Talata da ta gabata, inda Japan ta ce tana da bukatar kara kaimin daukar matakai na tsaro, domin ta tinkari, abin da ta kira, yanayi na karin matsalar rashin tsaro, wato barazanar da take fuskanta daga Jamhuriyar Damokuradiyyar Jama'ar Korea, da kasar Sin da kuma Rasha.

Kakakin ma'aikatar harkokin tsaron kaasr Sin, Yang Yujun, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewar, takardar dai na dauke ne da bayanai kan tsarin nan dake bayyana wasu batutuwa bisa radin kai, kan ayyukan tsaro da ci gaban ayyukan sojin kasar Sin.

Shi dai takardar ta soki kasar Sin game da abin da ta kira rashin fayyace al'amura game da ayyukan sojinta. Haka zalika a nashi bangare, Yang ya kuma zarge ta da yada farfaganda game da batun kafa yankin tsaron sararin sama a gabashin tekun Sin, da kuma dauki ba dadin baya bayan nan tsakanin jiragen saman sojin Sin da na kasar Japan.

ya zargi kasar Japan game da yayatawar da ta yi na cewar, ta kafa wani zango tsaro na tantance harkokin tsaro na jiragen sama a kudancin tekun kasar Sin, da kuma arangamar da aka yi tsakanin jiragen saman sojoji na Sin da na Japan.

Rahoton na kasar Japan ya kuma nuna cewa, ana fuskantar barazana daga kasar Sin domin kawai ya ruda kasashen duniya, Yang ya ce, ko kadan Sin ba za ta amince da hakan ba, kuma tuni kasar Sin ta rubuta takarda nuna kin amincewa zuwa kasar Japan.

Yang ya jaddada cewar, a kokarin da kasar Sin take yi na tafiyar da ci gabanta a cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, tana amfani da manufofi na kare kanta, kuma kamar yadda ya ce, Sin na da 'yanci na maida sojojinta na zamani ba tare da wani kace–nace ba.

Yang ya ce, matakan da sojojin kasar Sin ke dauka a cikin teku da kuma a samaniya, wani abu ne dake bisa tsarin doka.(Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China