Gwamnatin kasar Sin da Birtaniya sun fidda wata haddadiyar sanarwa, wadda ta shafi dangantakar dake tsakanin Sin da Birtaniya a fannoni masu yawa.
Wannan sanarwar da aka fitar a birnin London mai kunshe da sassa 30, ta bayyana karfin da dangantakar sada zumunci tsakanin kasashen ke da ita, musamman a fannin manyan tsare-tsaren hadin gwiwa da ya kasance wani muhimmin kashi cikin manufofin diplomasiyyar kasashen biyu.
Sanarwar ta ce a matsayin kasashen na abokan juna, sun sanya zarafi mai kyau na samun bunkasuwa tare. Baya ga kudurinsu na amincewa da bunkasa mu'ammala tsakanin manyan shugabanninsu, da ingiza hadin kai a fannoni daban-daban, da ma batun ba da jagoranci ga karfafa dangantakar dake tsakaninsu.
Kazalika kasashen biyu, suna darajanta ci gaban da aka samu cikin wasu tsare-tsaren tuntubar juna tsakanin manyan jami'ai, ciki hadda ganawa tsakanin firaministocinsu a wannan shekara, da tattaunawa a fannin tattalin arziki da ciniki, da tsarin yin musanyar ra'ayi kan al'adu, da bayyana ra'ayi bisa manyan tsare-tsare da dai sauransu, matakin da ake fatan zai taimaka wajen bude karin hanyoyin habaka wadannan tsare-tsare.
Bugu da kari kasashen biyu sun amince da shirya tattaunawa a karo na 6, a fannin tattalin arziki da hada-hadar kudi tsakaninsu, a watan Satumbar dake tafe a kasar Birtaniya. (Amina)