in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojan ruwa na Sin da na Namibia sun yi atisayen soja kan teku a karon farko
2014-06-11 16:02:01 cri
Tawagar 16 ta sojan ruwan Sin dake bada kariya ga jiragen ruwa ta yi atisayen soja tare da sojojin ruwan kasar Namibia a tekun dake dab da mashigin tekun Walvis na kasar Namibia, wannan ne karo na farko da kasashen biyu suka yi atisayen soja.

Muhimman ayyukan da suka gudana a yayin atisayen sojan su ne musanyar dabarun aiki tsakanin bangaririn biyu bisa halin da ake ciki da sadarwa da sauransu, kuma an gudanar da wannan atisayen sojan cikin nasara.

Mai bada umurni na rundunar sojan Sin Li Pengcheng ya bayyana cewa, ta wannan atisayen soja, an kara fahimta da imani da juna a tsakanin sojojin ruwan kasashen biyu, kana yana da babbar ma'ana a fannonin kara hadin gwiwar aikin soja a tsakaninsu da inganta karfin yaki da 'yan fashin teku tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China