in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da shugaban Congo-Brazzaville
2014-06-13 20:42:54 cri
A yammacin yau Jumma'a 13 ga wata ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban Congo-Brazzaville, Denis Sassou-Nguesso.

A yayin ganawar, Li ya bayyana cewa, gwamnatin Sin tana sa kaimi da nuna goyon baya ga kamfanonin Sin da su shiga aikin gina hanyoyin jirgin kasa da yankunan musamman a fannin tattalin arziki a Congo-Brazzaville, tare da zuba jari kan sha'anin kere-kere a kasar. Kuma Sin tana fatan taimakawa kasashen Afirka wajen gina hanyoyin jiragen kasa da na samamota,da filayen saukar jiragen sama, da kuma samar musu da jiragen sama, kuma na mota ta yadda za a iya hade nahiyar waje guda da bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka tare cikin sauri. Bugu da kari, Sin za ta samar wa kasar Congo-Brazzaville da sauran kasashen Afirka fasahohinta na samun bunkasuwa domin sa kaimi ga bunkasa nahiyar Afirka cikin zaman lafiya da lumana, tare da tabbatar da hadin gwiwa da samun moriyar juna tsakaninsu.

A nasa bangare, shugaba Sassou ya furta cewa, Congo-Brazzaville tana nuna godiyarta ga kasar Sin bisa taimakon da ta ke ba ta cikin dogon lokaci. Tana fatan zurfafa hadin gwiwa tsakaninta da Sin a dukkan fannoni,sannan tana maraba da zuwan kamfanonin Sin a kasar, domin samun bunkasuwa tare .(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China