in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar sojin ruwan Sin za ta kai ziyara a Afirka ta Kudu
2014-06-16 10:40:35 cri
Bisa gayyatar da sojojin ruwan kasar Afirka ta Kudu suka yi mata, tawaga ta 16 ta sojojin ruwan Sin mai bada kariya ga jiragen ruwa, za ta gudanar da ziyara a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu, tun daga ranar 17 zuwa 20 ga watan nan na Yuni da muke ciki.

Wannan ne dai zango na karshe da tawagar sojojin ruwan ta Sin za ta kai ziyara a nahiyar Afirka, kana shi ne karo na biyu da sojojin ruwan Sin suka kai ziyara a Afirka ta Kudu.

Jakadan Sin dake kasar Afirka ta Kudu Tian Xuejun ya bayyana cewa, a yayin ziyarar, tawagar za ta yi mu'amala tare da sojojin ruwan kasar Afirka ta Kudu, kana jama'ar kasar za su kalli wannan ganawa. Mr. Tian ya yi imani cewa wannan ziyara, za ta kara bunkasa fahimtar juna, da sada zumunci a tsakanin kasashen biyu, tare kuma da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin sojojin kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China