in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan karfafa dangantaka da jamhuriyar Congo
2014-06-14 16:32:18 cri

Shugaban Majalissar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang, ya ce kasarsa na fatan karfafa dangantakar dake tsakaninta da jamhuriyar Congo, domin cimma burin bunkasa hadin gwiwa da kawance dake tsakanin sassan biyu.

Zhang wanda ya bayyana hakan jiya ranar Jumma'a, yayin ganawarsa da shugaba Denis Sassou Nguesso na jamhuriyar Congo wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin, ya kara da cewa, karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen 2 buri ne da zai haifar da nasarori masu yawa a fagen samar da ci-gaba, da na cimma moriya da taimakawa juna.

Kaza lika shugaban majalissar ta NPC ya ce manufofin kasar Sin suna kama da na jamhuriyar Congo, musamman a fagen kokarin bunkasa ci-gaban kasashen.

Shi kuwa a nasa jawabi shugaba Sassou cewa ya yi, cikin shekaru 50 da kafa huldar kawance tsakinin kasarsa da Sin, dangantakar dake tsakaninta yi matukar yaukaka. Sassou ya ce, kasarsa za ta ci gaba da daukar matakan duk da suka dace, wajen ganin an fadada abota tsakanin jamhuriyar Congo da kasar Sin a dukkanin fannonin ci-gaba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China