An dai gudanar da taron karo na 24 na kasashen da suka amince da yarjejeniyar dokar zaman lafiya a teku ta MDD, a cibiyar MDD a ranar Litinin, domin murnar cika shekaru 20 da daddale wannan yarjejeniya.
Yayin taron shugaban tawagar Sin Wang Min, ya bayyana cewa, yarjejeniyar ta tabbatar da tsarin doka da oda a kan teku, wadda ta samu amincewa daga kasa da kasa. Ya ce cikin shekaru 20 da suka gabata, yarjejeniyar da hukumar kula da harkokin karkashin teku, da kuma kotun kula da dokar teku ta duniya suke aikin zartaswa ta samu nasarori da dama.
Bugu da kari Mr. Wang Min ya jaddada cewa, kasar Sin kasa ce da ke bin dokokin tekun kasa da kasa, tana kuma fatan warware kataddamar da ta shafi hakan cikin lumana. Gwamnatin kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar diplomasiyya mai kunshe da zaman lafiya, da bin ka'idojin kundin tsarin MDD, da na yarjejeniyar dokar teku, da warware rikicin teku cikin lumana, da kuma girmama hakkin kasa da kasa na zabin hanyar zaman lafiya don warware rikici. Hanya mafi kyau wajen warware rikici a kan teku dai ita ce, kasashen da rikicin ya shafa su gudanar da shawarwari, bisa tushen girmama tarihi, da dokokin kasa da kasa, kuma wannan ita ce nasarar da yawancin kasashe suka samu a wannan fanni. (Zainab)