in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Birtaniya za su kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama
2014-06-12 14:46:17 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang zai kai ziyarar aiki a kasar Birtaniya, ziyarar da za ta ba shi damar ganawa da firaministan Birtaniya a hukunce. Ziyarar dai da ake shirya gudanarwa ta biyo bayan gayyatar da firaministan kasar Birtaniya David Cameron ya yi masa.

A cewar karamin jakadan ofishin kula da harkokin kasuwanci na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar ta Birtaniya Zhou Xiaoming, yayin ziyarar ta Li Keqiang a Birtaniya, kasashen biyu za su kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa masu yawa, da za su shafi fannonin sha'anin kasuwanci, da hanyar sadarwa ta yanar gizo, da al'adu, da tashar samar da wutar lantarki ta haske rana, da kuma nazari kan harkokin magunguna da dai sauransu.

Mr. Zhou ya kara da cewa, ziyarar firaminista Li Keqiang a kasar Birtaniya, za ta ciyar da hadin gwiwar kasashen biyu a fannin tattalin arziki da kasuwanci gaba. Kana yarjejeniyoyin da kasashen biyu za su kulla a wannan karo, za su shafi fannoni da dama cikin hada wasu sabbin fannonin da a baya ba a taba yin hadin gwiwa game da su ba.

Bugu da kari Zhou ya bayyana cewa, kasashen Sin da Birtaniya za su ci gaba da inganta huldar cinikayyar dake tsakaninsu, bisa fannoni daban daban cikin 'yanci kamar yadda suka saba yi, duba da yadda suke mai da hankali sosai kan matsayin su a harkokin kasa da kasa. Tuni kuma suka tuntubi juna da hadin kansu, wajen inganta shawarwarin Doha karkashin kungiyar cinikayya ta WTO, da daidaita manufofin cinikayya, da nazari kan kafuwar yankin cinikayya cikin 'yanci tsakanin Sin da kasashen Turai da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China