in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Rasha sun gabatar da sabon daftarin ka'idoji da ya shafi sararin samaniya
2014-06-11 15:06:58 cri
A ranar 10 ga wata a gun cikakken taron tattaunawa kan batun kwance damara a birnin Geneva, kasar Sin da Rasha sun gabatar da sabon daftarin ka'idojin hana ajiye makamai da aikin soja a sararin samaniya, kana sun bada shawarar kafa wata sabuwar doka ta hanyar yin shawarwari domin hana gasar jan damara da ma amfani da makamai a sararin samaniya.

A gun taron, manzon Sin mai kula da harkokin kwace damara Wu Haitao ya bayyana cewa, bisa dokar da ta shafi sararin samaniya ta yanzu, ba ta iya hana yin amfani da makamai a sararin samaniya, kana ba ta iyar magance kai hari kan abubuwan dake sararin samaniya ba.

Wu Haitao ya kara da cewa, Sin da Rasha suna son saurarar shawarwari daga bangarori daban daban domin kyautata wannan daftarin, don aza tubali wajen fara yin shawarwari a wannan fanni a gun taron. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China