in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana matsayinta kan rahoton da Amurka ta fitar game da harkokin sojan kasar Sin
2014-06-11 20:41:05 cri
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Geng Yansheng ya yi jawabi a ran 11 ga wata kan rahoton da Amurka ta fitar kan halin da Sin ke ciki a fannin harkokin soji da tsaro. A cikin jawabinsa, ya ce, rahoton da Amurka ta fitar tsoma baki ne kan tsare-tsare sojin da Sin ke gudanarwa da ayyukan raya harkokin sojojinta don neman dacewa da zamanin da kasar take ciki, inda Amurka ta ce wai sojojin kasar Sin za su kawo barazana kuma Sin ta rufe hakikanin halin da sojinta ke ciki yanzu, haka kuma ta yi korafe-korafe kan wasu batutuwan da suka shafi harkokin cikin gidan kasar Sin, ciki hadda batun yankin Taiwan, sararin teku da tsaron yanar gizo ta Intanet, shata sassan tsaron sararin samaniya na Tekun Gabas da dai sauran fannoni. Kakakin ya ce Sin na nuna matukar rashin jin dadinta kan wannan mataki na Amurka. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China