in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira da a kiyaye wani tsarin sararin teku mai jituwa
2014-06-11 20:29:49 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying ta bayyana a yau Laraba 11 ga wata cewa, Sin na goyon bayan yarjejeniyar dokar teku na kasa da kasa da kuma warware rikici kan sararin teku cikin lumana.

A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Madam Hua ta yi bayanin cewa, an kira taron musamman na kasashen da suka daddale dokar teku ta MDD karo na 24 a birnin New York a ran 9 ga wata, domin bikin cika shekaru 20 da daddale wannan yarjejeniya. Shugaban tawagar Sin kuma mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Wang Min ya ba da jawabi a taron, inda ya yi kira da a kafa wani tsari dangane da teku mai jituwa tare da goyon bayan kasashen da rikicin teku ya shafa da su yi shawarwari kai tsaye domin daidaita matsalarsu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China