Taron na wannan karo dai ya maida hankali ga tattauna nasarorin da FAO, da ma sauran kasashen duniya suka samu yayin da ake aiwatar da hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa a fannin aikin gona. Har ila yau an nazarci hanyoyin da ya dace a bi a wannan fanni a nan gaba. Cikin jawabin da ya gabatar yayin taron, mataimakin ministan harkokin aikin gona na kasar Sin Chen Xiaohua ya ce, rashin tsaro a fannin abinci na haddasa rashin daidaito yayin da ake kokarin samun bunkasuwa a duniya, yana kuma kawo illa ga samun bunkasuwar tattalin arziki, da zaman lafiya a duniya. Don haka, ya zama tilas al'ummomin duniya su yi hadin gwiwa da juna don tinkarar wannan kalubale.
Haka nan Mr. Chen Xiaohua ya ce, kamata ya yi kasashen duniya su dauki nauyin dake wuyansu mabambanta, su kuma taimakawa kasashe masu tasowa wajen bunkasa aikin gona da tabbatar da tsaron abinci. (Zainab)