A cewar mista Xie Zhenhua, tun daga shekarar 2011, gwamnatin kasar Sin ta kara mai da hankali kan hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashe masu tasowa domin tinkarar sauyin yanayi, kuma ta kebe kudi dalar Amurka miliyan 11 a ko wace shekara don ba da gudummawa da goyon baya ga sauran kasashe masu tasowa ta hanyar samar musu kayayyakin tsimin makamashi, don rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, tare kuma da daga matsayinsu na tinkarar sauyin yanayi. (Zainab)