in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kara fahimtar manufar kasa daya, tsarin mulki biyu ta hanyar gabatar da takardar bayani
2014-06-11 15:15:09 cri
Gwamnan yankin musamman na Hong Kong Leung Chun Ying ya yi wa 'yan jarida bayani a ranar 10 da wata da yamma game da takardar bayanin da ta shafi manufar kasa daya, tsarin mulki iri biyu a yankin musamman na Hong Kong da gwamnatin Sin ta fitar cewa, ta wannan takarda, al'ummar yankin Hong Kong da kasa da kasa za su kara fahimtar manufar kasa daya, tsarin mulki iri biyu da kuma yadda 'yan Hong Kong suke raya yankin da kansu.

Leung Chun Ying ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da wannan takardar bayanin da ta shafi manufar kasa daya, tsarin mulki iri biyu a ranar 10 ga wata, kuma wannan ne karo na farko da gwamnatin Sin ta fidda irin wannan takarda game da aikin yankin Hong Kong. A wannan rana kuma, gwamnatin yankin Hong Kong ta bayar da wata sanarwa, inda ta yi maraba da takardar da gwamnatin Sin ta gabatar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China