A cikin jawabinsa, Xi ya gabatar da bukatu 5 wajen sa kaimi ga yin kwaskwarima kan samar da kuma yin amfani da makamashi, na farko, sa kaimi ga yin gyare-gyaren yin amfani da makamashi, da yaki da amfani da makamashi ta hanyar da ba ta dace ba. Na biyu, sa kaimi ga yin kwaskwarima kan samar da makamashi, da bullo da hanyoyi daban daban na samar da shi, da sa kaimi ga yin amfani da kwal yadda ya kamata, da kara kokarin bunkasa makamashi da ba na kwal ba, domin samar da wani tsarin makamashi da ya hada da kwal, da man fetur, da iskar gas, da makamashin nukiliya, da sabon makamashi, da makamashin da za a iya sake amfani da shi baki daya. Na uku, sa kaimi ga yin kwaskwarima ga fasahohin makamashi, domin daga matsayin wannan sha'ani. Na hudu, sa kaimi ga yin kwaskwarima ga tsarin makamashi, domin bullo da wani tsarin kasuwanni da ake iya yin takara a ciki. Na biyar, karfafa hadin gwiwa da sauran kasashen duniya daga dukkan fannoni, da tabbatar da tsaron kasar a fannin makamashi bisa yanayin da Sin take ciki na bude kofa ga kasashen waje.(Fatima)