Mr. Zhao ya ce, akwai dadadden zumunci tsakanin kasar Sin da kasar Equatorial Guinea, kuma cikin 'yan shekarun nan an kara karfafa fahimtar juna kan harkokin siyasa, an kuma samu kyawawan sakamako mai yawa, duba da yadda kasashen biyu ke kyautata hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa.
Zhao ya ce kasar Sin na fatan ci gaba da kyautata hadin gwiwarta da kasar Equatorial Guinea, tare da ba da taimako ga jama'ar kasar wajen cimma burinsu na neman bunkasuwa. Bugu da kari a cewarsa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, tana fatan karfafa mu'amala da hadin gwiwarta tare da jam'iyyar dimokuradiyyar kasar Equatorial Guinea, don inganta bunkasuwar tattalin arziki, da zamantakewar al'umma, ta hanyar karfafa kwarewarsu wajen gudanar da ayyukansu.
Mr. Ecoro ya bayyana cewa, kasar Sin abokiyar arzikin kasar Equatorial Guinea ce, kuma kasarsa na da burin ci gaba da mu'amalar jam'iyyoyin biyu, da karfafa hadin gwiwar kasashen biyu bisa moriyar juna, ta yadda za a iya ba da babbar gudumawa ga bunkasuwar kasashen. (Maryam)