Shugaba Xi ya jaddada cewa, Sin za ta yi kokarin kyautata dangantaka tsakaninta da kasashen Afirka, da nuna goyon baya ga kasashen Afirka da su daidaita matsalolinsu da kansu, da kara ba da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwar nahiyar Afirka. Dadin dadawa, Sin na fatan sa kaimi gainganta sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da kasashen Afirka zuwa wani sabon mataki tare dabisa hadin kai da kasar Congo Brazzaville.
A nasa bangare, Shugaba Sassou-N'guesso ya bayyana cewa, Congo kasarsa na fatan karfafa hadin gwiwa tsakaninta da Sin, da sa kaimi ga jerin ayyukan hadin gwiwa, kuma tana maraba da zuwan kamfanonin Sin domin zuba jari a bangaren bunkasa albarkatun ma'adinai, da gina muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, da raya yankin musamman a fannin tattalin arziki. Congo na fatan karfafa mu'amala tsakaninta da Sin cikin a fannin harkokin MDD.(Fatima)