in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta mika takarda ga MDD game da matsayinta kan sabanin ta da Vietnam
2014-06-10 10:40:20 cri
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wang Min, ya mika wata takarda ga magatakardar MDD Ban Ki-moon, game da batun dasa shinge ga ayyukan kamfanin kasar Sin a kan teku da kasar Vietnam ta yi, yana mai bukatar Mr. Ban da ya rawa wannan sako ga sauran kasashe mambobin MDD.

Bayan gabatar da wannan takarda mai taken "ayyuka a rijiyoyin hakar mai masu lamba 981: tsokana da Vietnam ta yi da kuma matsayin Sin kan batun", Mr. Wang ya bayyana wa 'yan jarida cewa, burin Sin shi ne, ta gabatarwa duniya matsayinta tare da bayyana hakikanin lamarin.

Haka zalika Mr. Wang ya jaddada cewa, tun fil azal yankin tsibiran Xisha yanki ne na kasar Sin, babu kace-nace ne kan wannan batu . Ya kuma yi fatan kasar Vietnam za ta yi la'akari da dangantakar dake tsakaninta da Sin, da batun zaman lafiya a yankin tekun na kudu, da girmama ikon mallakar kasar Sin, da kuma dakatar da dasa shinge ga ayyukan kamfanin Sin, da janye jiragen ruwa da ma'aikatansu daga yankin ba tare da bata lokaci ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China