Babban daraktan hukumar ta FAO Jose Graziano da Silva ne ya bayyana hakan yayin wani taron hukumar, yana mai cewa an tsara muradan karni na shekarar 2000 ne a gun taron koli na MDD na shekarar 2000, inda cikinsu aka sanya batun rage yawan mutane masu fama da yunwa a duniya ya zuwa rabi, tun daga shekarar 1990 zuwa 2015.
Koda yake bisa kididdigar da FAO ta yi, an ce kasar Sin ta cimma burin rage yawan mutane masu fama da yunwar tun ma kafin cikar wannan wa'adi.
Mr Silva ya ce, a matsayin wata babbar kasa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen yin kokarin cimma burin. Nasarorin Sin za su kawo karfi da fasahohi ga sauran kasashen duniya wajen yaki da matsalar yunwa.
Don gane da wannan ci gaba mataimakin ministan harkokin aikin gona na kasar Sin Chen Xiaohua, ya bayyana wa 'yan jarida cewa kasar Sin za ta yi kokari, wajen jan hankulan jama'a game da cin abinci mai gina jiki. Mr. Chen ya ce ban da kokarin tabbatar da tsaron abinci a gida, kasar Sin tana bada gudummawa ga kasashen waje a wannan fanni, tare da goyon baya ga hadin gwiwa da kasashe masu tasowa a fannin aikin gona, tuni kuma ta riga ta tura masana a harkar aikin gona fiye da dubu daya zuwa kasashe daban daban, baya ga horar da kwararru fiye da dubu 30 a sauran kasashen duniya. (Zainab)