An yi bikin rantsuwar Abdelfattah al Sisi a matsayin sabon shugaban kasar Masar a Lahadin nan, bayan da kotun kolin kasar ta tabbatar da nasarar da ya samu yayin babban zaben kasar da ya gabata.
A jawabin sa jim kadan da rantsuwar kama aikin, shugaba Sisi ya yi alkawarin biyayya ga dokokin kasar, tare kuma da baiwa manufofin cimma moriyar jama'a cikakkiyar kulawa. Sisi ya ce zai tabbatar da kiyaye 'yancin kasar, da cikakkun yankunan ta.
A ranar 3 ga watan nan na Yuni ne dai kwamitin kolin zaben kasar ta Masar, ya sanar da sunan tsohon shugaban rundunar sojin kasar Abdelfattah Al-Sisi, a matsayin mutumin da ya lashe zaben da ya gabata, da kuri'u da yawansu ya kai kashi 96.91 cikin dari na daukacin kuri'un da aka kada, lamarin da ya bashi nasara kan abokin takararsa dake da sassaucin ra'ayi Hamdeen Sabbahi. (Amina)