Ministan kula da harkokin yawon shakatawa na kasar Masar Hisham Zaazou ne ya bayyana hakan, yayin da ya gana da wata tawagar Sinawa mai mutum 350 da ta ziyarci wurin shakatawa na Hurghada da ke bakin tekun Bahar Aswad a lokacin bikin bazara.
Ministan da Jakadan kasar Sin da ke Masar Song Aiguo da kuma Gwamnan yankin Bahar Aswad sun yi tattaki zuwa Hurghada don tarbar wannan tawaga ta Sinawa, inda suka nuna musu ni'imtattun wurare da na tarihi na kasar Masar da kuma raye-raye kasashen biyu.
Minista Zaazou ya ce, kimanin Sinawa masu yawan bude ido 3,000 ne suka ziyarci kasar ta Masar tun daga ranar 30 ga watan Janairun 2014, inda ya ce, yana fatan ganin karin Sinawa sun kawo ziyara kasar ta Masar a nan gaba.
Ya ce, kasar Masar ta yaba wa kokarin da jakadan Sin dake Masar ya yi wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa a Masar ta hanyar hadin gwiwa da ma'aikatar al'adu.
A nasa jawabin jakada Song, ya ce yana fatan Sinawa masu yawon shakatawa za su yi amfani da abubuwan da suka gani a Masar bayan sun koma gida Sin.
Ya kuma bayyana cewa, a mako mai zuwa ne, za a ci gaba da shagulgulan da aka tsara gudanarwa a birnin Alkahira dangane da bikin barazana, inda ake maraba da Misriwa da dukkan Sinawa da ke kasar ta Masar. (Ibrahim)