Babban kwamitin rundunar sojojin kasar Masar (CSFA) ya bada amincewarsa a ranar Litinin ga ministan tsaron kasar Masar, Abdel Fatah al-sisi, kuma shugaban rundunar sojojin kasar, don ya shiga takarar zaben shugaban kasar Masar a wani labarin da kamfanin dillancin labaran kasar MENA da shafin internet na Ahram suka bayar.
Haka kuma kwamitin ya amince da murabus din mista Al-sisi daga mukaminsa na shugaban rundunar sojojin kasar in ji MENA tare da cewa shugaban rundunar sojojin kasar zai yi bayani a cikin 'yan sa'o'i masu zuwa idan zai shiga takarar zaben shugaban kasar ko a'a. (Maman Ada)