Game da ra'ayin babban sakataren MDD kan hakan, Farhan Haq ya ce, Ban Ki-Moon ya goyi bayan ra'ayin wannan ofishi, zai kuma ci gaba da mayar da hankali kan batun.
Ban da wannan kuma, ofishin ya bayyana cewa, abin da aka fi damuwa da shi shi ne, kame mutane sama da dubu bisa ta'addanci da ake musu tun cikin watan Yulin bara.
A ranar 24 ga watan nan ne dai kotun lardin Minya dake kudancin kasar ta Masar, ta yanke wa mambobin kungiyar 'yan uwa Musulmi, da masu goyon bayan kungiyar 528 hukuncin kisa, sakamakon zargin su da kaiwa ofishin 'yan sanda farmaki, matakin da ya haddasa mutuwar 'dan sanda guda, a wata zanga-zanga da aka yi a watan Agustan bara. (Bilkisu)