Ibrahim Mahlab wanda ya yi murabus daga mukamin ministan gidaje na gwamnatin wucin gadi a ran 24 ga wata Fabrairu da ya gabata, ya karbi umurnin sabon shugaban kasar na kafa wata sabuwar gwamnati nan take. Bayan shawarwari da ya yi tare da 'yan takara a cikin mako daya da ya gabata, Ibrahim Mahlab ya gabatarwa shugaban kasar Adly Mansour takardar jerin sunayen ministocinsa. Bisa labarin da kafar yada labarai a wurin ta bayar, an ce, takardar ba ta kunshi sunayen wasu manyan ministoci ba ciki hadda ministan tsaron kasar,don haka shugaba shi zai yanke shawara kan wannan abu.
An ba da labari cewa, sabuwar gwamnati tana kunshe da ministoci 31, biyar daga cikin su na rike da mukamai biyu, wato ministan matasa da na motsa jiki, ministan tsare tsare da na hadin kai da kasa da kasa, ministan masana'antu da na zuba jari da cikini, ministan ilmi da na nazarin kimiyya, ministan raya harkokin kasa da na raya yankunan kasa.
Mambobin sabuwar gwamnati a wannan karo babu babban sauyi idan aka kwatanta da wanda ya gabata. Bisa labarin da shafin yanar gizo na Internet na kasar ya bayar an ce, tsoffin ministoci 20 na mulkin Hazem Al-Beblawi sun zama sabbin ministocin sabuwar gwamnatin. (Amina)