in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar za ta shirya babban zaben shugaban kasa kafin zaben majalisar dokoki
2014-01-27 10:37:13 cri

A ran 26 ga wata, shugaban wucin gadi na kasar Masar Adly Mansour ya yi wani jawabi a gidan talibijin, inda ya sanar da cewa, Masar za ta shirya babban zaben shugaban kasa kafin zaben majalisar dokoki.

Malam Mansour ya yi kira ga kwamitin koli na kula da harkokin zabe da ya ba da tabbaci ga 'yan takaran babban zaben shugaban kasa da su yi rajista da shiga yakin neman zabe.

A watan Disamba na bara, bayan da ya gama aikin yin gyara kan tsarin mulkin kasa, kwamitin kula da harkokin gyaran tsarin mulkin Masar ya bayyana cewa, sabon kundin tsarin mulkin kasar bai tabbatar da odar gudanar da babban zabe da zaben majalisar dokoki ba.

A ran 14 da 15 ga wata, Masar ta gudanar da zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar, a karshe dai an zartas da daftarin da samun kuri'un amincewa kashi 98 bisa dari. Amma jama'a kashi 40 bisa dari kawai sun je kada kuri', yayin da sauran jama'a ba su amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar ba.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China