in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata kotu a Masar ta yanke ma magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi 528 hukuncin kisa
2014-03-24 20:56:51 cri
Wata kotun manyan laifuka a kasar Masar a yau Litinin din nan 24 ga wata ta yankewa magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmai su 528 hukuncin kisa dangane da laifin kai hari ga ofisoshin 'yan sanda a babban gundumar kasar na Minya a watan Agustan bara, kamar yadda kafar talabijin din Nile ta rahoto.

Magoya bayan kungiyar dai ana zargin su da kai hari a kan wani dan sanda a yankin Mattai tare da kashe mataimakin shugaban 'yan sanda wannan yankin lokacin da ake kokarin ta da 'yan zanga zanga masu kama wuri zauna na nuna adawar su da sauke shugaba Morsi.

Kotun ta kuma salami wadansu 17. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China