Sakatare janar ya nuna goyon bayansa ga mutanen kasar Masar da su tabbatar da makomarsu kan wannan lokacin na wucin gadi cikin zaman lafiya da adalci, in ji wannan sanrawa. Tun ranar Talata har zuwa ranar yau Laraba, 'yan kasar Masar ke zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki. Masar ta dukufa wajen tafiyar mulkin wucin gadi bisa tsarin demokaradiyya tun faduwar shugaba Hosni Mubarak bayan boren 'yan kasar. A watan Yulin da ya gabata, rundunar sojojin kasar ta hambarar da shugaba Mohamed Morsi, suka dakatar kundin tsarin mulki, sannan suka kafa gwamnatin wucin gadi.
Mista Ban ya yi kira ga 'yan kasar Masar da su bayyana ra'ayinsu ta hanyar zaman lafiya, tare da nuna cewa, MDD za ta cigaba da tallafawa tsarin da 'yan kasar ke bi dake zuwa daidai da tsarin demokaradiyya wanda ke ba da damar fadin albakacin baki da 'yancin 'dan adam a cikin wannan kasa. (Maman Ada)