in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada Sedki Sobhi a matsayin ministan tsaron kasar Masar
2014-03-28 11:11:22 cri
Shugaban rundunar sojojin kasar Masar, janar Sedki Sobhi ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon ministan tsaron kasar, inda ya maye gurbin Abdel-Fattah al-Sissi da yin murabus domin shiga takarar zaben shugaban kasa mai zuwa, in ji kafar talabijin din kasar.

Shugaban wucin gadi, Adli Mansour ya kara wa Sobhi lambar girma a matsayin laftana janar a ranar Laraba, wani mataki na shirya shugaban rundunar sojojin wajen maye gurbin mista Sissi bisa kujerar ministan tsaron kasar.

Mista Sissi ya bayyana takararsa a zaben shugaban kasa a ranar Laraba 26 ga wata a cikin wani jawabi ta kafar talabijin dake bayyana wani burbushin yakin neman zabe, tare da yin alkawarin dukufa domin kare Masar daga ta'addanci da kuma gina kasa bisa tsarin demokaradiyya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China