in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun nuna damuwa kan hukuncin kisa da Masar ta yanka daruruwan magoya bayan Morsi
2014-04-29 11:04:35 cri

A ran 28 ga wata, wata kuton hukunta manyan laifuffuka ta kasar Masar ta yanke mambobin kungiyar 'yan uwa Musulmi da magoya bayan jam'iyyar da yawansu ya kai 683 hukuncin kisa, ciki har da tsohon shugaban jam'iyyar Mohamed Badie. Zargin da ake masu sun hada da laifuffukan nuna karfin tuwo, rura wutar gaba, kone-kone da lalata hukumomin 'yan sanda tare da kisan 'yan sanda, a yayin zanga-zangar shekarar bara. Yanzu haka hukuncin kisa da Masar ta yanka ya jawo hankulan kasashen duniya.

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da wata sanarwa ta kakakinsa, inda ya nuna babbar damuwa ga hukuncin kisa da Masar ta yanke wa mambobin kungiyar 'yan uwa Musulmi da magoya bayansu da yawansu ya kai 683.

Ban Ki-moon ya ce, mai yiyuwa ne wannan hukuncin da Masar ta yanka zai kawo babbar illa ga shiyyarta da tsaron kasar, domin zaman karko a Masar yana da muhimmanci matuka ga duk shiyyar arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya.

Haka shi ma, shugaban kasar Turkiya Abudllah Gul ya bayyana a birnin Ankara cewa, yana fata Masar za ta iya soke hukuncin kisa da ta yanke wa mambobin kungiyar 'yan uwa Musulmi da magoya bayansu da yawansu ya kai 683. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China