Wata kotun bincike manyan laifufuka da ke yankin kasar Masar ta sanar da yankewa mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi MB da masu goyon bayansu baki daya mutane 683 hukuncin kisa a ran 28 ga wata, ciki hadda tsohon shugaban kungiyar Mohamed Badie.
Bisa labarin da gidan telibijin na kasar Masar ya bayar an ce, wadannan mutane fiye da 600 da suka gurfana a gaban kotun ana thumar su da aikata laifin yin amfani da karfin tuwo, tada gobara, kashe 'yan sanda da kutsa kai cikin ofisoshin da sauransu.
A wannan rana kuma, wannan kotu ya sake binciken hukuncin kisan da aka yankewa mambobin kungiyar 529 a baya, daga cikinsu mutane 37 ba a canja hukuncin da aka yanke musu ba, inda aka yanke wa sauran 492, hukuncin daurin rai da rai. (Amina)