A ran 16 ga wata, kamfanin dillancin labarun gwamnatin kasar Masar MENA ya rawaito cewa, kwarya-kwaryan sakamkon da aka samu ya nuna cewa, fiye da kashi 90 bisa dari na kuri'un da aka samu na maraba da sabon kundin tsarin mulkin kasar Masar.
Da misalin karfe 9 na dare na ranar 15 ga wata bisa agogon wurin, an kammala zaben raba gardama kan sabon daftarin tsarin mulkin kasar Masar, wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa. A halin yanzu dai, an ci gaba da aikin kidayyar kuri'un da aka kada.
An ce, a cikin kwanaki biyu na wannan zabe kan sabon daftarin tsarin mulki, an samu zaman karko a yawancin yankunan kasar, amma a wasu wurare an samu rikici, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9, tare da jikkata mutane fiye da 10. (Danladi)