Tsohon babban hafsan sojojin kasar Abdel Fattah al-Sisi wanda ya jagoranci tumbuke gwamnatin Morsi da jagoran masu ra'ayin mazan jiya Hamdeen Sabahy ne kawai za su fafata a zaben.
Al-Sisi ya kara samun farin jini tun lokacin da ya hambarar da Morsi a watan Yulin da ya gabata,bayan boren gama garin da aka yiwa gwamnatinsa ta shekara guda,abin da ake ganin zai taimaka masa cikin sauki wajen samun galaba a kan Sabahy, mutumin da ya zo na uku a zaben shugaban kasar na shekarar 2012. (Ibrahim)