in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dage sauraron karar da ake yiwa Morsi
2014-02-02 15:53:36 cri
Rahotanni daga kasar Masar na cewa, kotun hukunta masu aikata manyan laifuffuka ta kasar Masar, ta dage sauraron karar da ake yi wa hambararren shugaban kasar Masar Mohamed Morsi da ake zargi da turzura tashin hankali da kashe masu zanga-zanga zuwa ranar 4 ga watan Fabrairu.

Lauyoyin da ke kare Morsi, sun bukaci kotun da ta dage shari'ar domin su samu karin lokacin nazartar muhammin takardun da suka shafi karar.

Lauyan Mohamed Morsi Sileem al-Awaa ya bayyana cewa, babu gaskiya a shari'ar, domin an yanke masa hukunci ne a bayan kejin gilashin da aka garkama shi a ciki, wanda ya ce ya saba wa dokokin yanke wa shugabannin hukunci.

Ana zargin Mohammed da wasu 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi 14 da tayar da fitina da kashe masu bore a wajen fadar shugaban kasa a watan Disamban shekarar 2012, bayan da aka bayar da sanarwar ayyana kundin tsarin mulkin kasar da ake takaddama a kai, wanda ya baiwa shugaban cikakken iko, boren da ya yi sanadiyar rayukan mutane 8.

Bugu da kari, ana tuhumar tsohon shugaban kasar ta Masar ta laifin fasa gidan yari, cin amanar kasa da cin mutuncin bangaren shari'a.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA, ya bayyana cewa, da safiyar ranar Asabar ne wani jirgin sama mai saukar ungulu ya dauko Mohamed Morsi daga gidan yarin Borg al-Arab da ke birnin Iskandariya

zuwa dakin taron cibiyar horas da sanda da ke gabashin birnin Alkahira, inda aka jibge jami'an tsaro yayin sauraron karar.

Shari'ar da aka yi wa Morsi ta ranar Asabar, ita ce ta bayyanarsa ta uku a bainar jama'a, tun lokacin da sojoji suka tumbuke shi daga karagar mulki tare da garka me shi a gidan kaso a farkon watan Yulin shekarar da ta gabata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China