Shugaba Xi Jinping ya ce, kasar Masar ita ce kasa ta farko cikin kasashen Afirka da Larabawa da suka kulla dangantakar diflomasiyya da kasar Sin, kuma dangantakar kasashen biyu na ci gaba da bunkasa cikin yanayi mai kyau cikin shekaru 58 da suka gabata ne aka kulla dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Masar. Kuma kasar Sin za ta ci gaba da bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare kuma cikin dogon lokaci, tana fatan ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Masar wajen zurfafa dadadden zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen biyu, karfafa hadin gwiwa kan fannoni daban daban, ciyar da hadin gwiwar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare gaba, don tallafawa kasashen biyu da kuma al'ummominsu (Maryam)