A kalla mutane 8 ne suka rasa rayukan su, yayin da wasu mahara suka kai farmaki kan ginin majalisar dokokin kasar Somaliya, dake birnin Mogadishu.
Tuni dai kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Al-Shabaab, mai alaka da Al-Qaeda ta sanar da daukar alhakin harin da aka kai da tsakar ranar jiya Asabar.
An ce dai wata maotao ce shake da boma-bomai ta tarwatse a kofar ginin majalissar, kafin daga bisani daya dagawasu maharan ya suka kutsa kai cikin ginin, inda ya suka yi musayar wuta da dakarun rundunar tsaro.
Wani jami'in tsaron kasar Mohammad Tahir ya tabbatar cewa, jami'an tsaro sun yi musayar wuta da mayakan, sun kuma killace 'yan majalisar.
Haka nan kafar yada labarum birnin ta ce, 'yan majalisa fiye da 100 ne ke tsaka da ayyukan su yayin da aka kai harin, inda nan take suka tsere, lamarin da ya sanya wasu daga cikin su samun raunuka.
Bugu da kari kafar ta ce an harbe mayaka 4 ko 5, yayin da kuma jami'an tsaro 4 suma suka rasa rayukan su. Sai dai wannan majiya tace mafi yawan wadanda suka jikkata fararen hula ne.
A wani ci gaban kuma babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da aukuwar wannan hari, ya na mai jaddada wajibcin dakile ta'addanci, ta hanyar daukar du duk wani mataki da ya dace. (Amina)