Nicholas Kay ya fadi haka ne ga kafofin yada labaru, yayin da ya halarci shawarwari kan batun kasar Somaliya da hukumar kare hakkin dan Adam ta shirya a birnin Geneva. Inda ya ce, cikin 'yan lokutan da suka wuce, kungiyar Al-shabaab ta sha kai hare-hare da dama, cikinsu har da harin da ta kai ga ofishin M.D.D. da ke kasar Somaliya, yanzu,wannan barazana ta shafi kasashen duniya. M.D.D. tana ganin ya kamata a yi kokarin yaki da kungiyar ta hanyar soji da siyasa kuma bisa halin da ake ciki.
Nicholas Kay ya ce, batun tsaro ya zama babban kalubale da kasar Somaliya ke fuskanta, idan ba a iya warware batun tsaro ba, ba za a samu nasara game da yunkurin siyasa na kasar Somaliya da sake gina kasar ba, sabo da haka, ya kamata kasashen duniya su kara nuna goyon baya game da rundunar tsaro ta Somaliya.(Bako)