Sanarwar ta ce birnin na Buula Burde wanda ke yankin Hiraan ya fada hannun dakarun dake biyayya ga gwamnatin kasar mai ci ne da yammacin ranar Alhamis, matakin da a cewar wakilin musamman na kungiyar AU, kuma jagoran tawagar AMISOM a Somaliyan Mahamat Saleh Annadif, wani babban ci gaba ne ga burin da ake da shi, na farfado da zaman lafiya da tsaro a kasar.
Buulu Burde dai ya zamo birni na 6 da tsagin gwamnatin kasar Somaliyan ya kwace cikin makwanni biyun baya bayan nan daga ikon kungiyar ta Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaida, birnin da kuma ke da matukar muhimmanci ga kungiyar ta fuskar sansani da samar da kayayyakin bukata ga dakarun kungiyar. (Saminu Hassan)