A ran 8 ga wata, kungiyar Al-Shabaab ta kasar Somaliya ta kai harin boma-bomai da aka dasa cikin mota a birnin Mogadishu, hedkwatar kasar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, yayin da wasu suka jikkata. Kwamitin sulhu na MDD ya nuna goyon baya ga kasashen duniya da mahukuntan kasar Somaliya wajen kawar da barazanar kungiyar kishin islama ta Al-Shabaab.
Dadin dadawa, kwamitin sulhu na MDD ya nanata cewa, ko wane irin ta'addanci na kasancewa tamkar barazana mai tsanani ga zaman lafiya da tsaron duniya. Harin ta'addancin da duk wanda ya kai bisa ko wane irin dalili a ko ina kuma ko yaushe, laifi ne ke nan, kuma ya zama tilas a gurfanar da shi a gaban kotu.
A sabili da haka, kwamitin sulhu na MDD ya yi aniyar yaki da ko wane irin ta'addanci bisa kundin tsarin mulkin MDD.(Fatima)